Abuja: shirin kafa rundunar ecowas
Abuja: shirin kafa rundunar ecowas"
Play all audios:
Yayin taron ministocin kula da harkokin kasashen waje da na tsaro na kasashen kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO din dai, sun bukaci kara kaimi wajen
yaki da ta'addanci da sasanta rigingimun siyasa da ake fuskanta a wasu kasashen kungiyar. Taron karkashin kwamitin tsaro da shiga tsakanin na kungiyar da ke kokari na samar da rundunar
tsaro ta shirin ko-ta-kwana a tsakanin, ya mayar da hankali ne a kan muhimmman batutuwa guda biyu da suka fi daukar hankali wato na dabarar da za su yi wajen bullowa barazanar da ayyukan
ta'adanci ke ci gaba da yi da kuma rigigimu na siyasa da wasu kasashen kungiyar suka afka da ya haifar da 'yan gudun hijira. Taron dai ya zo a kan gaba, domin kuwa an gudanar da
shi ne dai dai lokacin da ake kawo karshen shirye-shiryen da kungiyar ta yi na shawo kan matsaloli na aiyyukan ta'adanci a yankin da ta zama tamkar wutar daji da ta watsu zuwa kasashe
da dama. Kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO ta dade tana shirin samar da rundunar tsaro ta shirin ko-ta-kwana, wanda tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da
Burkina Faso ake kai kawo kansa. Har yanzu kungiyar ba ta fitar da rai ba wajen amfani da lalama domin maido da kasashen da suka fice daga cikinta, saboda dawo da sojojin da suka kifar da
dimukurdiyya zuwa cikinta. Kokarin da kasashen ke yi dai ya samu tagomashi daga Majalisar Dinkin Duniya, inda jakadan sakatare janar na majalisar a kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO da yankin
Sahel Leonardo Simao ya bayyana cewa za ta ci gaba da taimakawa domin samar da zaman lafiya da bunkasa dimukurdiyya da mulki na gari da kyautata zamantakewa ta hanyar mayar da hankali a kan
karfafa tattalin arzikin mata da matasa. Wannan shi ne karo na 54 da ake gudanar da wannan taro, kuma duk matsayar da suka cimma game da kudin da ake bukata da ma kasashen da za su bayar da
sojoji a kan fara aikin rundunar shirin ko ta kwanan za a gabatar da su ne a gaban shugabanin kungiyar da zasu yi taro a karshen mako a Abujar.
Trending News
Jam'iyyar apc ta kauce wa barazana ga makomartaDuk da cewar an dauki lokaci ana musayar yawu har ma an kai ya zuwa tashin kura, masu tsintsiyar tarayyar Najeriya, sun ...
naseem makiya | TechCrunchSAVE $200+ ON YOUR TECHCRUNCH ALL STAGE PASS BUILD SMARTER. SCALE FASTER. CONNECT DEEPER. JOIN VISIONARIES FROM PRECURSO...
Abuja: shirin kafa rundunar ecowasYayin taron ministocin kula da harkokin kasashen waje da na tsaro na kasashen kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen ...
Sanya Richards-RossCelebrityPersonSanya Richards-RossSanya Richards-Ross Is Pregnant! The RHOA Star Expecting Baby No. 3 with Husband Aaron...
Shaqiri shines as Bayern brush aside BATEThe 21-year-old Swiss international's performance was the high point for Bayern who fielded a mainly second-string team ...
Latests News
Shinto shrine hut in kyoto by kengo kuma‘hojo-an’ by kengo kuma, shimogamo-jinja shrine, kyoto prefecture, japanall images courtesy of kengo kuma kengo kuma pay...
Hadarin mota ya halaka mutane sama da 20 a cote d'ivoreHukomomin kasar Cote d'Ivore sun tabbatar da mutuwar mutane 21 tare da jikkatar wasu 10, sanadiyyar hadarin mota da...
"Mata-mata" no hexagonalO hexagonal semifinal do catarinense chega à sua metade neste meio de semana com três times em vantagem na briga pelas d...
Pompson SHI | Premiere.frBiographie News Photos Vidéos Films Séries Nom de naissance SHI Genre Homme Avis PoorNot so pooraveragegoodvery good Vid...
Siriya ta yi sulhu da kungiyoyi masu dauke da makamaiKungiyoyin da ke dauke da makamai a Siriya sun cimma yarjejeniya a wannan Talata da sabbin hukumomin kasar, wadda ta jib...