Jaridun Jamus: 20.12.2024 – DW – 12/20/2024

Dw

Jaridun Jamus: 20.12.2024 – DW – 12/20/2024"

Play all audios:

Loading...

Jaridar ZEIT ONLINE a sharhinta mai taken: ECOWAS ta sallama wa  Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso, kasashe uku da sojoji suka kifar da gwamnati tare da ayyana fita daga kungiyar ta


kasashen Afirka ta yamma a watan Janairun wannan shekara. Jaridar ta ce shugabannin kungiyar habaka tattalin arzikin Kasashen Afirka ta yamma ECOWAS ko CEDEAO, sun magantu a kan wannan


matsala, bayan kusan shekara guda suna ta kokarin samo mafita. Sun yanke shawarar kyale kasashen uku su kama gabansu, wannan babban koma-baya ne. A ranar Lahadin karshen makon da ya gabata


kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO ta amince da jadawalin fitar kasashen ku daga cikinta, inda a yanzu za a tabbatar da ficewar kasashen a hukumance a ranar 29 ga watan Janairun da ke tafe na


shekara ta 2025.  Shugaban Hukumar ECOWAS din ko CEDEAO Omar Touray ne ya sanar da hakan, inda ya ce kasashen na Mali da Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso za su kammala fita daga cikinta a


watan Yuli shekarar ta 2025. Ita kuwa mujallar FAZ NET ta rubuta sharhinta ne mai taken: Amfani da biliyoyin kudin zinare wajen daukar nauyin yaki. A Sudan ana fama da mummunan yaki da bai


kamata al'ummomin kasa da kasa da Jamus zu zuba ido suna kallo ba, ya kamata a ce tuni sun dauki matakin ladabtarwa ga bangarorin da ke yaki ta hanyar kakaba musu takunkumi kan muhimmin


abin da ke samar musu kudi shiga. Jaridar ta ce lamari na kara rincabewa a Sudan, sojojin gwamnati da dakarun 'yan tawaye na RSF na ci gaba da kaddamar da munanan hare-hare. Duka


bangarorin biyu sun saba tanade-tanaden dokokin kasa da kasa, wadanda suka wajabta kare rayukan fararen hula. A yanzu haka ba kasar da al'ummarta ke tserewa gidajensu da ke warwatse a


cikin kasarsu kamar Sudan a duniya, inda aka kiyasta sun kai sama da mutane miliyan 14 a yanzu ba ya ga wasu miliyan 12 da suka warwatse tun bayan barkewar yaki a watan Afrilun 2023. A yanzu


haka kuma sama da rabin al'ummar kasar na fama da matsananciyar yunwa, kiyasi ya nunar da cewa sama da mutane miliyan 25 wannan matsala ta shafa. Ita kuwa jaridar DIE TAGESZEITUNG ta


rubuta sharhinta ne mai taken: Rashin samun taimako bayan mahaukaciyar guguwa a unguwar talakawa ta Mayotte, har yanzu ko gawarwakin wadanda suka mutu yayin ibtila'in ba a kai ga ganowa


ba. Mozambik ma ta fada cikin bala'i, bayan mahaukaciyar guguwar da aka yi wa lakabi da "Chido" ta afku a yankin Mayotte a Tsibirin Comoros da ke karkashin ikon Faransa a


gabar ruwan Tekun Indiya, a yanzu ta isa Mozambik. A nan ma ta yi mummunar barna, kamar yadda rahotanni suka nuna. Rahotannin farko da suka fito daga hukumar kare afkuwar bala'o'i


ta Mozambik a ranar Talatar da ta gabata sun nunar da cewa, kimanin mutane 34 suka halaka yayin da sama da gidaje 20 suka rushe. Faifen bidiyo na farko da ya fito daga Mozambik din ma, ya


nuna yadda mahaukaciyar guguwar ta lalata gidaje a gundumar Cabo Delgado da ke yankin arewacin kasar. A wannan yanki ne dai mayaka masu ikirarin jihadi suka kwashe tsawon shekaru suna kai


hare-hare a kan sojoji, abin da ya janyo dubban mutane uska kauracewa gidajensu tare da zama a sansanonin 'yan gudun hijira na cikin gida. Ba mu karkare da jaridar NEUE ZÜRCHER ZEITUNG


da ta rubuta sharhinta mai taken, gasar tseren motoci na shirin komawa Afirka. Ruwanda ta nemi daukar nauyin babbar gasar ta Grand Prix, yayin da Afirka ta Kudu ta Marokko ba su da


kyakkyawan fata. A ta bakin Alexander Wurz da ke zaman shugaban kungiyar direbobin tseren motoci kana tsohon dan wasan tseren motocin na Ostiriya, tuni shirye-shiryen gasar ta Ruwanda ta dau


harami bayan da ya kwashe tsawon lokaci yana san ya idanu a Kigalin. A makon da ya gabata Shugaba Paul Kagame na Ruwandan, ya mika takardar neman daukar nauyin gasar ta Formula 1 da kasarsa


ke son daukar nauyi. Wannan mataki dai zai tabbatar da lakanin da ake wa kasar na "kasar dubban tuddai." Ko da yake har ynazu Ruwandan kyakkyawan fata kawai take da shi, amma


akwai yiwuwar gudanar da babbar gasar da ake kira da Grand Prix a Kigali.


Trending News

SARR ISMAILA | Premiere.fr

Biographie News Photos Vidéos Films Séries Nom de naissance ISMAILA Avis PoorNot so pooraveragegoodvery good Vidéo à la ...

Lebanon: 'yan gudun hijira na komawa

Masu komawa gidan dai na ta lissafin irin dimbin asarar da suka tafka daga rikicin Isra'ilar da kungiyar Hezbollah ...

Hadarin mota ya halaka mutane sama da 20 a cote d'ivore

Hukomomin kasar Cote d'Ivore sun tabbatar da mutuwar mutane 21 tare da jikkatar wasu 10, sanadiyyar hadarin mota da...

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tsagaita wuta a Zirin Gaza

Tsagaita wutar wadda Majalisar Dinkin Duniyar ke cewa ta dindindin ce, ta kuma kunshi batun sakin wadanda ake garkuwa da...

Google doodle: wer war mostafa el-abbadi?

Am heutigen Montag, dem 10. Oktober 2022, veröffentlichte die Internet-Suchmaschine Google erneut ein sogenanntes Google...

Latests News

Jaridun Jamus: 20.12.2024 – DW – 12/20/2024

Jaridar ZEIT ONLINE a sharhinta mai taken: ECOWAS ta sallama wa  Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso, kasashe uku d...

Google doodle: wer war mostafa el-abbadi?

Am heutigen Montag, dem 10. Oktober 2022, veröffentlichte die Internet-Suchmaschine Google erneut ein sogenanntes Google...

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tsagaita wuta a Zirin Gaza

Tsagaita wutar wadda Majalisar Dinkin Duniyar ke cewa ta dindindin ce, ta kuma kunshi batun sakin wadanda ake garkuwa da...

Hadarin mota ya halaka mutane sama da 20 a cote d'ivore

Hukomomin kasar Cote d'Ivore sun tabbatar da mutuwar mutane 21 tare da jikkatar wasu 10, sanadiyyar hadarin mota da...

Lebanon: 'yan gudun hijira na komawa

Masu komawa gidan dai na ta lissafin irin dimbin asarar da suka tafka daga rikicin Isra'ilar da kungiyar Hezbollah ...

Top